Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a jiya Laraba cewa, shugaba Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi ta hanyar faifan bidiyo, a yayin bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na hudu (CIIE) da kuma taron tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao.
Za a gudanar da bikin bude taron ne a birnin Shanghai ranar 4 ga watan Nuwamba, in ji mai magana da yawun Gao Feng.
Lokacin aikawa: Nuwamba-03-2021